YADDA ZAKA KORI SAURO
Dukda yanayin sanyi da ake ciki amma mutane suna kokawa akan yawaitan sauro tareda yin ƙorafi akan illolin da wasu magungunan kashe sauro ke haifarwa. 🌲 Ga wasu hanyoyi da mutum zaibi ya yaƙi sauro ba tareda wata illa ba. 👇 1- Asamu ɗanyen ɓawon lemo (lemon tsami kona zaƙi) da Albasa sai a busar dasu (amfiso a busar a inuwa) idan sun bushe sai a haɗa a adaka adinga zubawa a gaushi a hayayyaƙa ɗaki da duk inda sauro suke. 2- Ahaɗa Fatan lemon da Albasar a markaɗasu ko a dakasu sosai azuba ruwa kaɗan a gauraya atace sai a dinga yayyafawa inda sauro suke. 3- Asamu garin Habbatussauda da ɓawon Tafarnuwa (wanda ya bushe) sai a zuba a gaushi a hayayyaƙa ɗaki da duk inda sauro suke. 4- Asamu ganyen Taba-taba a busar dashi (a inuwa yafi) sai marmasasu adinga zubawa a gaushi ana hayayyaƙa ɗaki da duk inda sauro suke. 5- Asamu Lemon grass a busar dashi (a inuwa yafi) sai a adinga zubawa a gaushi a hayayyaƙa inda sauro suke. 6- Asamu lemon tsami a yayyakashi (slice) sai a haɗa da ƙw...