ALKUBUS DIN FULAWA๐✍️
KAYAN HADI(Ingredient) (1)FULAWA (2)Yeas (3) gishiri kadan (4)Ruwan (5)mai kadan YADDA ZA'A HADA Dafarko Zaki gyara fulawa wato ki tankade saboda ko da dadti sai asamu mazubi a zuba fulawa,yeas, gishiri kadan,mai kadan sai a samu ruwan mai dan dumi musamman idan lokaci sanyi zaifi sauran tashi, sai ki kwaba su dashi .kwabin yafi na fanke kauri sosai,sai asa arana ko kusa da dumin wuta a barshi yayi kamar minti 15 yadda Zai tashi sosai sai asami gwan-gwani ko leda ko kuma robobin zamani nayi alala ko alkubus ya dangan ta dabin da kike dashi sai a shafa mai kadan acikin gwangwanin saboda kar ya kama .Sai a zuba ruwa akasan tukunya ajera gwan-gwani aciki arufe sosai yadda turiri bazai fitaba ya turara shikenan. Anaci da Miya kalala kamar miyar alayyahu,miyar taushe,miyar zogale,miyar kwai.