ALALAN GURJIYA๐ฎ✍️
KAYAN HADI Gujjiya Manja Tattasai Albasa Gishiri Attaruhu Magi Curry Ledar Santana Ruwan YADDA ZA'A HADA -Da farko za'a nika gujjiya tayi laushi sosai sai a tankade acire tsaki -A zuba manja a cikin garin gujjiya sai akwaba da hannu Sannan a zuba tafashashshen ruwa ba mai yawa ba ,akwaba sosai da ludayi -Sai a zuba markadadden tattasai ,albasa,da attaruhu da Kori da gishiri da kayan dandano -A zuba ruwa har sai kaurin kullin yayi daidai yadda ake so -A zuba hadin a leda sai a kulla yadda ake so -Sai a Dora tukunya a turarashi kamar yadda ake alala.