URIC ACID DA MAGANIN SA
URIC ACID. DA MAGANINSA MINENE URIC ACID? Uric acid wani sinadari ne da ake samunsa a cikin jini ta hanyar cin wasu nau'ika abinci masu dauke da sinadarin "purine" mai yawa. Hakka kan janyo hauhawar uric acid din wadda ke bi ta cikin koda kuma hakan yana da nasaba da yanayin aikin Koda. Idan ya kasance kodar bata iya sarrafa wannann sinadarin ta hanyar fitar da shi a fitsari, to mutum zai gamu da jinyar hauhawar uric acid. Idan sinadarin uric acid ya yi yawa a jikin mutum, ya kan taruwa a gabobi, gwiwowi da duga-dugan mutum ya haifar da ciwon rikewar gabobin ko gwiwowi wato "Gout" a turance. Sannan ya Kan haifar da ciwon Koda samfurin "Kidney stones" idan ba a dauki mataki ba. Sannan zai haifar da dawwamammen ciwon gabobi da gwiwowi da Kuma lalata tsokar da ke kewaye da gabobin. ALAMOMIN WANNAN CIWO: 1. Ciwon Gwiwowi 2. Zafin kafafu 3. Ciwon Duga-Dugai 4. Ciwon Ga6o6i ABUBUWAN DA KE JANYO HAUHAWAR SINADARIN 1. Yawan Amfani da "sea ...