Posts

Showing posts with the label YADDA AKE DASHISHI ๐Ÿฝ️✍️

Yadda ake dashishi ✍️

Image
Dafarko za'a tanadi kayan yi dashishi .Alkama,mai fari ba manjaba,gishiri kadan,Ruwa.A fara da gyara Alkama sai a tsince ta a surfa ta a cire dusar.Awanke ta abari ta bushe,sai a barzo ta amma kada tayi gari sosai.A zuba ruwa a tsame ta yadda barjin zai yi laushi idan an turara shi,har sai yafara cuccurewa,Daga nan sai a zuba mai da gishiri a jiya sosai amma a sauke Kuma asaka mai yadda zai warware daga cuccurewa,a kara mayarwa kan wuta.Idan yayi za'a ji yana kamshi shikenan sai a kwashe a zuba a mazubi. Ana iya ci da miyar ganye ko taushe ko Kuma irin miyar da ake so.