KAMSHIN JIKI ๐บ✍️
HADIN KAMSHI (1) Lalle Madarar turaren sandal bakhur Madarar turaren ledus Madarar turaren musk Da farko a zuba lalle a tukunya asa ruwa ,a Dora a wuta ya dahu sosai ,sai a sauke , a tace duddugar lallen Sai a mayar ruwan lalle kan wuta ,a rage wuta sai a kawo madara turaren sandal bakhur,da madarar turare ledus da madarar turare musk,sai a barsu su tafasa,sannan a sauke,in ya huce a nemi jarka ko wani mazubi mai murfi a juye a cikin,duk sanda a kayi wanka aka gama sai a zuba wanan hadin shi kadan acikin bokiti asa masa ruwa kadan sai a dauraye jiki da shi ,kar a goge abarshi ya bushe,yadda kamshin zai kama jiki. HADIN KAMSHI (2) Kafin amarya qamshi Garin ambar Garin miski Kafun-kafun Sai a cakudasu a cikin bassilin (Vaseline) a rings shafawa .Duka inda kika je to gurin zai dinga qamshi sosai.