KAMSHIN JIKI ๐ŸŒบ✍️

HADIN KAMSHI (1)
Lalle
Madarar turaren sandal bakhur
Madarar turaren ledus
Madarar turaren musk
Da farko a zuba lalle a tukunya asa ruwa ,a Dora a wuta ya dahu sosai ,sai a sauke , a tace duddugar lallen
Sai a mayar ruwan lalle kan wuta ,a rage wuta sai a kawo madara turaren sandal bakhur,da  madarar turare ledus da madarar turare musk,sai a barsu su tafasa,sannan a sauke,in ya huce a nemi jarka ko wani mazubi mai murfi a juye a cikin,duk sanda a kayi wanka aka gama sai a zuba wanan hadin shi kadan acikin bokiti asa masa ruwa kadan sai a dauraye jiki da shi ,kar a goge abarshi ya bushe,yadda kamshin zai kama jiki.

HADIN KAMSHI (2)
Kafin amarya qamshi
Garin ambar
Garin miski
Kafun-kafun
Sai a cakudasu a cikin bassilin (Vaseline) a rings shafawa .Duka inda kika je to gurin zai dinga qamshi sosai.

Comments

Popular posts from this blog

GAMASU BUKATAR AIKIN NGO GA DAMA๐Ÿ‘‡