ALALAN GURJIYA๐Ÿฎ✍️

KAYAN HADI
Gujjiya
Manja
Tattasai
Albasa
Gishiri
Attaruhu
Magi
Curry
Ledar Santana
Ruwan
YADDA ZA'A HADA
-Da farko za'a nika gujjiya tayi laushi sosai sai a tankade acire tsaki
-A zuba manja a cikin garin gujjiya sai akwaba da hannu Sannan a zuba tafashashshen ruwa ba mai yawa ba ,akwaba sosai da ludayi
-Sai a zuba markadadden tattasai ,albasa,da attaruhu da Kori da gishiri da kayan dandano
-A zuba ruwa har sai kaurin kullin yayi daidai yadda ake so
-A zuba hadin a leda sai a kulla yadda ake so 
-Sai a Dora tukunya a turarashi kamar yadda ake alala.

Comments