ALKUBUS DIN FULAWA๐Ÿš✍️

KAYAN HADI(Ingredient)
(1)FULAWA
(2)Yeas
(3) gishiri kadan 
(4)Ruwan
(5)mai kadan
YADDA ZA'A HADA
Dafarko Zaki gyara fulawa wato ki tankade saboda ko da dadti sai asamu mazubi a zuba fulawa,yeas, gishiri kadan,mai kadan sai a samu ruwan mai dan dumi  musamman idan lokaci sanyi zaifi sauran tashi, sai ki kwaba su dashi .kwabin yafi na fanke kauri sosai,sai asa arana ko kusa da dumin wuta a barshi yayi kamar minti 15 yadda Zai tashi sosai sai asami gwan-gwani ko leda ko kuma robobin zamani nayi alala ko alkubus ya dangan ta dabin da kike dashi sai a shafa mai kadan acikin gwangwanin saboda kar ya kama .Sai a zuba ruwa akasan tukunya ajera gwan-gwani aciki arufe sosai yadda turiri bazai fitaba ya turara shikenan.
Anaci da Miya kalala kamar miyar alayyahu,miyar taushe,miyar zogale,miyar kwai.

Comments

Popular posts from this blog

GAMASU BUKATAR AIKIN NGO GA DAMA๐Ÿ‘‡