YADDA ZAKA KORI SAURO


Dukda yanayin sanyi da ake ciki amma mutane suna kokawa akan yawaitan sauro tareda yin ƙorafi akan illolin da wasu magungunan kashe sauro ke haifarwa.


🌲 Ga wasu hanyoyi da mutum zaibi ya yaƙi sauro ba tareda wata illa ba. 👇


1- Asamu ɗanyen ɓawon lemo (lemon tsami kona zaƙi) da Albasa sai a busar dasu (amfiso a busar a inuwa) idan sun bushe sai a haɗa a adaka adinga zubawa a gaushi a hayayyaƙa ɗaki da duk inda sauro suke.


2- Ahaɗa Fatan lemon da Albasar a markaɗasu ko a dakasu sosai azuba ruwa kaɗan a gauraya atace sai a dinga yayyafawa inda sauro suke.


3- Asamu garin Habbatussauda da ɓawon Tafarnuwa (wanda ya bushe) sai a zuba a gaushi a hayayyaƙa ɗaki da duk inda sauro suke.


4- Asamu ganyen Taba-taba a busar dashi (a inuwa yafi) sai marmasasu adinga zubawa a gaushi ana hayayyaƙa ɗaki da duk inda sauro suke.


5- Asamu Lemon grass a busar dashi (a inuwa yafi) sai a adinga zubawa a gaushi a hayayyaƙa inda sauro suke.


6- Asamu lemon tsami a yayyakashi (slice) sai a haɗa da ƙwayar Tafarnuwa (bayan an ɓare) sai a watsasu inda sauro sukafi yawa.


7- Asamu Tafarnuwa a ɓare sai a jajjaga azuba ruwa ƙadan adafa sai a tace adinga yayyafa ruwan ko asa a spraying bottle adinga fesawa inda sauro suke.


Comments

Popular posts from this blog

GAMASU BUKATAR AIKIN NGO GA DAMA👇