MAZA KUYI HAKURI IYA MATA KAWAI
A samu 6awon kankana, sai a rinka goge fuska
da shi yana gyara fuska tayi sumul.
✨HADIN GYARAN JIKI
Wannan hadin shine hadi na, musamman
wanda yake sa fatar mace tazamo tana tare da shauki
da laushi kai harma kaji jikinta yana wani damshi
damshi
a. Lemon tsami
b. Tatacciyar madara
c. Kwa guda (1)
Ki sami ayaba mai kyau ki Bare ko ki matse da
hannunki, ko ki markada ya yi laushi, sai ki zuba
tatacciyar madara ki fasa Kwai kamar guda daya,
amma farin zaki zuba, sai ki matse lemon tsami ki
gauraye shi ki shafa a jikinki ya samu kamar tsayin
awa daya, sai ki yi wanka da ruwan zafi.
Idan kika lazimci yin haka kamar kwana uku
zaki sha mamaki.
(1)✨GYARAN FATA
a. Lemon tsami
b. Bawon kwai
c. Kur-kur
Zaki hade su guri guda ki daka su sai ki rinka wanka
dashi, fatar mace zata goge ta yi kyawun gaske.
(2)✨GYARAN FATA NA BIYU
Hadi na musamman wanda yake kama da maida
tsohuwa yarinya
a. Ayaba
b. Sabulun salo
c. Man auduga
d. Dudu osun (Sabulun Dudu Osun)
e. Dettol
f. Lemon tsami.
Zaki hae su gun d'aya, ki rinka wanka das hi fatarki
zata yi laushi da santsi,
(3)✨GYARAN FATA NA UKKU
a. Ganyen magarya
b. Sabulunsalo
Zaki daka ganyen magarya, sai ki zuba a cikin
Sabulun salo ki rinkawankayana gyarajiki.
GYARAN FATA NA HADU
a. Ganyen magarya
b. Man zaitun
c. Man habbatus sauda
Ana daka ganyen magarya a zuba cikin man zaitun
da man habbatus sauda shi ma yana gyarajiki.
(5)✨GYARAN FATA NA BIYAR
a. Lalle
b. Garin Ridi
Ana amfani da lalle kafin ki shiga wanka sai ki
waba ki zuba garin ridfi ki shafe jikinki zuwa awa
daya, sai kiyi wanka.
(6)✨GYARAN FATAN NA SHIDA
a. Man zaitun
b. Ridi
Zaki daka ridfi, amma sai kin gyara shi kin
shanya ya bushe sai ki daka ki zuba cikin man
zaitun. Idan zaki kwanta bacci sai ki shafe fuskar ki
dajikinki, da safe ki wanke zaki sha mamaki.
Comments