CUTAR DAKE KAMA MATA BAYAN HAIHUWA
KAR KA YI FUSHI DA MATARKA BAYAN HAIHUWA – GA DALILIN SA
Yana da muhimmanci ga maza su fahimci cewa bayan mace ta haihu, tana shiga wani sabon mataki na rayuwa wanda yake da nauyi sosai ga jikinta da zuciyarta. Ba wai kawai haihuwa ta kawo gajiya bane, amma tana iya haifar da wata matsala ta kwakwalwa da ake kira Postpartum Depression – wato ciwon damuwa bayan haihuwa.
Wannan yanayi yana faruwa ne sakamakon sauyin sinadarai (hormones) a jikin mace, gajiya daga nakuda da haihuwa, rashin samun bacci, da kuma sabbin nauyukan kula da jariri.
Idan kai mijin kirki ne, ya kamata ka gane cewa canjin halayenta a wannan lokaci ba laifinta bane, ba kuma saboda soyayyarta gareka ta ragu ba.
ALAMOMIN DA KAKE IYA GANI A WURIN MATARKA
1. Karancin kulawa gareka: Ba kamar da ba, bata nuna maka kulawa.
2. Soyayya ta ragu: Bata sake nuna kaunarka sosai.
3. Magana marar tunani: Duk abin da ya zo bakinta sai ta fada.
4. Bata damu da jariri ba: Zaka ga kamar bata damu da jaririn da ta haifa.
5. Bacin rai kullum: Kullum fuska cike da damuwa.
6. Maganar mutuwa: Zai iya zama ta fara cewa gara ta mutu ko ta huta.
7. Maganar saki: Batare da dalili ba sai ta fara cewa ka sake ta.
8. Rashin tsafta: Bata kula da jikinta ko gidan ba.
9. Mantuwa: Duk abin da aka fada mata sai tace ta manta.
10. Rashin bacci: Ko jaririn yana barci, itama bata iya yin bacci.
ABIN DA YA KAMATA MIJI YA YI
Ka kwantar mata da hankali: Kada ka dauki hakan da tsana ko fushi.
Ka nuna mata soyayya: Wannan lokaci tana bukatar soyayyarka fiye da kowane lokaci.
Ka taimaka mata a ayyukan gida: Kada ka bar duk wahala a kanta.
Ka saurareta: Ka barta ta fadi damuwarta, ka rungumeta da hakuri.
Ka kula da lafiyarta: Idan ka ga matsalar na tsananta, ku tafi asibiti domin neman shawarar likita.
MUHIMMAN SAKO
Wannan yanayi ba laifin mace bane, kuma ba alama bace cewa soyayyarta gareka ta gushe.
Abinda take bukata shi ne kulawa, fahimta, da taimakon aure.
Idan mijinta ya yi mata hakuri ya nuna mata soyayya, da taimako, tana warkewa cikin sauri.
Amma idan aka dauki lamarin da tsana ko zargi, matsalar na iya tsananta har ta shafi lafiyarta da lafiyar jaririn.
KARKAREWA
Dan uwa, aure amana ne. Ka kula da matarka bayan haihuwa domin ita da jaririn su samu lafiya. Idan ka nuna mata kulawa da tausayi, za ku cigaba da rayuwa cikin farin ciki.
๐บ Ka raba wannan rubutu domin wasu iyaye su amfana.
Comments