ABINDA KE FARUWA DA MAHAIFA BAYAN HAIHUWA

 Ko Kunsan Abin Da Ke Faruwa Da Mahaifa Bayan Haihuwa ๐Ÿฉธ? 


Daga Shafin Ciki da Raino


Yawancin mata kan fi mayar da hankali kan jariri bayan haihuwa, su manta da wani babban bangare da ke bukatar kulawa ta musamman wato "mahaifa" .


To, yar’uwata, bayan kin haihu, mahaifar ki tana cikin wani yanayi na gyara tare da dawowa yadda take a baya, kuma yana da matuฦ™ar muhimmanci ki san yadda hakan ke faruwa.


◾ Da farko, mahaifa tana raguwa a hankali daga girman da ta kai lokacin goyon ciki zuwa yadda take kafin ciki. Wannan tsari yana daukar makonni 6 zuwa 8, sai dai wasu suna fin wasu sauri. Wannan yana faruwa ne saboda jiki yana zubar da tsohon jini ta hanyar lochia — wato jinin bayan haihuwa.


◾ A kwanakin farko, wannan jini yana da ja mai duhu, kamar jinin haila, amma daga baya yana raguwa har ya koma kamar ruwa mai ษ—an rawaya.

๐Ÿ‘‰ Idan kin ga ya dawo da yawa ko ya fara wari, to hakan na iya zama alamar matsala — ki garzaya asibiti.


◾ A yayin wannan lokaci, mahaifa tana matsewa wanda hakan ke haddasa ciwon ciki ga masu jego. Wannan shi ake kira afterpains. Yana faruwa ne saboda jiki yana ฦ™oฦ™arin dawo da mahaifar yadda take kafin ciki. Ki sani, hakan alama ce mai kyau — yana nufin mahaifa tana warkewa.


◾ Kada ki manta da hutawa sosai, saboda jikin uwa yana bukatar lokacin murmurewa. Yin aiki da wuri, ko rashin samun hutu, yana iya janyo zubar jini mai yawa ko jinkirin dawowar mahaifa yadda take a farko. 


◾ Shan ruwa mai yawa, cin abinci mai gina jiki, da bin umarnin likita su ne sirrin saurin murmurewa.

Kuma idan kin ga jinin bai tsaya ba bayan makonni 6, ko kina jin wari, ko ciwon baya ya tsananta — kar ki yi shiru, ki tuntuษ“i likita.


Uwargida, ki kula da kanki kamar yadda kike kula da jaririnki, domin uwa mai lafiya ita ce ginshikin jariri mai lafiya. ๐Ÿ’š


Idan wannan bayani ya amfanar, ki raba shi domin wata uwa ma ta amfana.

Ko mayi tarayya a cikin ladan.

Comments

Popular posts from this blog

GAMASU BUKATAR AIKIN NGO GA DAMA๐Ÿ‘‡