HAKURI MATAKI NASARA ๐✍️
HAKURI :ibada ne Allah ya halicci Dan dam akan halaye dabam-dabam,don haka ake samu masu sauki da tsanani cikin mu'amalar mu ta yau da gobe.
Yana daga cikin shiriyar Annabi (S.A.W)an nusar damu neman tsarin Allah daga sharrin kawunan mu,da miyagun aiyuka mu,don haka duk Wanda zakayi mu'amala dashi to Yana iya maka dai-dai,kuma Yana iya yi maka kuskure.
Yana da wuya ace kullum sai anyi maka yadda kake so,ko sai kaji abinda zaiyi maka Dadi,ko sai idon ka yaga abinda zai faranta maka rai.Don haka rayuwa sai ka hada da hakuri akan komi.
'yan uwa mu sani ba Wanda zai zamo Mai hakuri face an bashi lada Mai yawa game da hakuri sa, mutuncin sa ya Karu,zama dashi zaiyi sauki da dadi, dabi'un sa zasu zamo abin sha'wa, kuma zai zamo abin misali nagari,kuma abin koyi ga kowa musamman zuriyar sa.
Hakuri Yana gyara zaman iyali,Yana karfafa zumunta, Yana maganin fitina da tashin hankali,Yana kawo sulhu da yafe laifi,yana gadar da halaye nagari, Yana inganta zaman makwabta, yana haifar da alheri Mai yawa a duniya da lahira.
Hakuri na lada shine Wanda ake yinshi don neman yarda Allah,da Wanda akayi shi ana cikin fushi ko damuwa,da hakuri abinda kana iya ramawa ko daukar fansa.lallai Allah Yana tare da masu hakuri, kuma anyi musu tanadi na lada Mai girma da aljannah a wajen ubangiji mu.
Comments