LABARAN SHEHU JAHA ๐✍️
Wata rana shehu jaha yana kan soron gidansa ๐ yana aiki sai ga wani almajiri๐ถmai bara ya zo wucewa sai ya daga kai sama ya hango shehu jaha yana ta aikinsa.Sai ya kwala masa kira yace"Kai malam sauko kaji wata magana"
Da shehu ya sauko ya zo wajen almajiri,sai almajiri yace ma shehu
"Kawo kunnen ka kaji๐"
Sai shehu ya mika masa kunnen sa ,
Sai almajiri ya rada ma shehu cewa
"Sadaka nake nema"
Sai shehu yace masa "to zo muje"
Sai almajiri ya biyo shi suka hau can
sama inda shehu yake aiki ,Sannan shehu yace masa "matso kaji๐wata
magana "Almajiri ya matso yaba shehu kunnen sa,sai shehu ya rada masa a kunnen ๐cewa"ba zaka samu ba".
NASAN WANNAN๐
Wata rana shehu jaha yaje wani gari๐ Kuma bai San kowa a garin ba,sai yaga wasu mutanane suna cin abinci๐sai ya tsoma masu hannu a cikin kwanon ya fara ci ๐,sai mutanen suka tambaye shi ,"waka sani a cikin mu??" Sai shehu yace "NASAN WANNAN" ya nuna ๐abinci๐.๐
GIDANMU SUKE NUFI๐ซ
Shehu da dansa suna zaune akofar gida suna hutawa.sai ga jama'a dauke da gawar mamaci zasu wuce ,acan karshen baya kuma wata mata ce ke tsalle tana tumuwa a kasa tana kururuwa kuka tana fadin cewa "yanzu megida shikenan za'a kaika gidan๐ซ da babu shimfida,ba katifa ๐️,babu gurasa๐ฅba zuma ๐ฏ".
Koda dan gidan shehu jaha yaji zantukan matar sai ya wai ways ya dubi uban nasa yace"Baba wallahi GIDANMU SUKE NUFI zasu kaishi".
Comments