DUNIYA MAKARANTA PART(1) 🌍✍️

(1)Kada ka zolayi 😝masu aikata zunubi.Dukanmu Muna cikin suturar Allah ne.Amma kayi musu nasiya da lafazi kyakkyawa.Duk masu laifi basu Kai fir'auna👽 ba,Kuma duk masu wa'azi 🎙️basu kai matsayin Annabi musa (Alaihis salam)ba .Amma Allah yace da shi :ka gaya ma fir'auna magana mai laushi,watakil zai karbi wa'azi ko yaji tsoron  Allah.

(2) A da can mutane basu da asibitoci 🏥.Amma suna da lafiya.Basu da yawan kudin💵amma akwai ilimi.Ba hanyoyi 🛣️sufuri dana sadarwa☎️Amma akwai zumunci.Basu da yawan ni'imomi,Amma suna da jin dadi😊.ko kun san dalili?"Albarkar abu tafi yawansa".

(3)Idan ka saka kudin💵a account ko ka cire kana samun alert na abin da ya rage ko ya karu a cikin jarinka.ina ma ace duk lokacin🕰️daka ci Naman Dan uwanka zaka samu alert na yawan zunubin ki?  KO Kuma idan kayi sallah ko azumi ko sadaka zaka samu alert na yawan ladan da ake baka ?A kullum ka aikata sabon ko sa'a haka tana faruwa ,Amma malai'ku ne suke lissafa maka suna rubutawa ✍️,kuma zasu hada rasitinka gaba daya a baka gobe kiyama,a buga total,A fitar da sakamako ,sannan a yanke hukunci .Allah kasa mushiga Aljanna Ameen🤲.

(4)yaro 🧑akwai lokacin 🕰️da karfi amma babu KUDI💵.Dattijo 🧔akwai kudi💵da karfi💪amma babu lokaci🕰️.Tsoho akwai kudi 💵 da lokaci 🕰️ amma babu karfi💪.A rayuwar in ka samu wani abu ne zaka rasa wani .Cikakkiyar ni'ima kawai tana aljanna.ya Allah kabamu Aljanna🤲 .

(6)Huda-huda🦅 tsuntsu ne daya kawo rahoto,ya isar da sako ,ya nuna kishin addinin sa .kada ka bari tsuntsu yafika son Allah da kishin addinin sa.

(7)Uwa 🧕ita kadai ce take manta kanta a Addu'ar🤲,ta shagaltu dayi ma danta👶.mu so❤️ iyayenmu muringa yi musu biyayya da addu'oi sanda suke raye da bayan ransu😭Allah kagafartawa iyayan mu Ameen🤲.

(8)Abokai 👬irin uku ne:
-mai sonka don kanka.
-Da mai sonka don Kansa.
-wanan Kuma yana tare da 
Kai ne idan ka samu.
Idan ka rasa zaiyi ko sama ko kasa
Zaka rasa shi.

(9)Sauki yana tare da tsanani.
Mai hakuri yana cim ma dadi.
Mai kyauta bays rasawa.kowa
Yaji tsoron Allah, Allah zai sama 
Masa mafita. Manta da damuwa
Ka fuskanci rayuwar.kowa ka gani
a duniya akwai abinda ya dame shi.

(10)Ba kowacce faduwa ce matsala ba.
Da yawa Wanda zai Fadi amma idan ya 
tashi ya 🏃sheka baka iya cimmasa.

(11)Da yawa mutanen da muka San su,
Muka yi hulda da su a yau sun riga mu gidan gaskiya.idan yau mune,wata rana 
ba mune ba.

(12)Da yawa Wanda kece ma 'ya'yansu :
"Ina son kazama likita👩‍⚕️,Ina son kama injiniya👩‍🔧,ina son kazama malami🕵️.
Mutum nawa ne su kace ma dansu :
Ina son ka zama mai Albarka🤲,Mai 
taimakon jama'a".

Comments

Popular posts from this blog

GAMASU BUKATAR AIKIN NGO GA DAMA👇